An Kona Gidan Shugaba Joseph Kabila

Shugaba Joseph Kabila

Wasu mahara a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Congo sun kona gidan gona mallakar shugaban kasar, Joseph Kabila kurumus a jiya Litinin kuma suka kashe wani dan sanda.

Kabila bashi a cikin gidan dake kusa da kauyen Musienene lokacin da aka kai farmakin, kuma har yanzu ba’a gano yanda aka kashe jami’in dan sandan ba.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin cinnawa gidan gonar wuta. Amma wani jami’in soja ya fadawa kampanin dillancin labaran Faransa cewa yana dora laifi a kan kungiyar mayakar Mai-Mai, yana cewar sun lalata gidan kafin suka konata.

Kasar DR Congo ta jima da abkawa cikin rudanin siyasa a kan kin amincewar shugaba Kabila ya sauka daga mulki.

Wa’adinsa na biyu kuma na karshe ya kare ne tun cikin watan Disemban 2016 saannan kuma an kasa iya gudanarda zaben da ya kamata a yi a cikin wannan shekarar 2017. An sake dakatar da zabe zuwa a kalla shekara guda nan gaba, lamarin da ya kara fusata kungiyoyin ‘yan banga na kasar.