An Makare Khashoggi Kafin Daddaza Gawarsa

Khashoggi

Wani mai bincike na musamman a Turkiyya ya ce an kashe ‘dan jaridar Saudiyar nan Jamal Khashoggi ne ta hanyar shakeshi, jim kadan bayan da ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya na Istanbul, kafin a daddatsa gawarsa.

Bayanin da mai binciken na musamman Ifran Fidan yayi, na zuwa ne lokacin da Turkiyya ke matsawa Saudiyya lamba ta mika mata mutane 18 da ta tsare saboda suna da hannu a kisan Khashoggi.

Bayanin Fidan, shine bayani na farko da wani jami’in Turkiyya yayi da ya tabbatar da cewa an kashe dan jaridar bayan da ya shiga ofishin jakadancin, kuma abu ne da aka riga aka shirya yi.

Haka kuma wani mai magana da yawun jam’iyyar AK mai mulki a Turkiyyya, ya fada jiya Laraba cewa, tabbas kisan Khashoggi ba zai taba yiwuwa ba, batare da izinin daya daga cikin shugabannin Saudiyya ba.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nemi jami’an Saudiyya su bayyana dan Turkiyya da ake zargi da taimakawa wajen boye ko jefar da gawar Khashoggi.