Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata a Hukunta Masu Hannu a Kisan Khashoggi - Erodgan


Yayin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ke jawabi a gaban majalisar dokokin kasar

A makon da ya gabata, hukumomin Saudiya suka amince cewa lallai Khashoggi ya mutu a cikin ofishin jakadancin, inda a farko suka bayyana cewa ya gamu da ajalinsa ne bayan wata tarzoma da aka yi.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya ce kisan dan jaridar kasar Saudiyya wanda kuma mazaunin Amurka ne, wato Jamal Khashoggi, lamari ne da aka shirya shi.

Ya kara da cewa ya kamata a hukunta wanda ya ba da umurnin kisan da kuma duk wanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Yayin wani jawabi da ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar a yau Talata, Erdogan ya bayyana yadda lamarin ya faru tun ana gobe Khashoggi zai shiga ofishin jakadancin Saudiyyan a Istanbul.

Ya kara da cewa, Saudiyya ta tura tawagogi da dama zuwa Istanbul domin su hadu da Khashoggi a ofishin jakadancin inda suka cire faifan na’urar daukan hoton wurin.

Erdogan ya kara da cewa, matar da Khashoggi zai aura, Hatice Centgiz, ta yi ta jira a wajen ofishin jakadancin na Saudiyya har na tsawon wasu sa’o’i, kafin daga bisani ta tuntubi hukumomin Turkiyya inda ta bayyana masu cewa an tsare Khashoggi ba bisa san ransa ba kuma rayuwarsa na cikin hadari.

A makon da ya gabata, hukumomin Saudiya suka amince cewa lallai Khashoggi ya mutu a cikin ofishin jakadancin, inda a farko suka bayyana cewa ya gamu da ajalinsa ne bayan wata tarzoma da aka yi.

Daga baya kuma suka sauya matsaya suka ce ya rasu ne sanadiyar shake shi da aka yi a lokacin da ya yi yunkurin ficewa daga ofishin domin neman dauki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG