An salami tsoshon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela daga asibiti

Motar da ta dauki tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela bayan an sallame shi daga asitin Milpark dake birnin Johannesburg, Jan 28, 2011

An salami tsoshon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela daga wani asibiti dake birnin Johannesburg bayan wata gajerar jinya.

An salami tsoshon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela daga wani asibiti dake birnin Johannesburg bayan wata gajerar jinya. Dan gwaggwarmayar yakin wariyar launin fata mai shekaru 92 ya bar asibitin Milpark zuwa gidanshi yau Jumma’a. An kwantar da shi ne a asibitin ranar Laraba domin abinda da farko ofishinsa ya bayyana a matsayin gwajin lafiyarsa. Kwanciyarshi a asibiti ya sa jama’a tababa kan koshin lafiyarshi. Babban likitan fida na asibitin Vejaynand Ramkalan ya bayyana yau jumma’a cewa, Mr. Mandela yana kara murmurewa, sai dai yace za a kara sa mashi ido. Mr. Mandela yana fama da rashin lafiya da ya hada da tarin fuka.