Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hosni Mubarak Ya Rusa Gwamnatinsa


Shugaban Hosni Mubarak na Masar,a jawabi da yayi wa al'umar kasar ranar Jumma'a.

A cikin jawabinda ya gabatar,shugaba Mubarak ya yi alkawarin kaddamar canji a harkokin siyasa da tattalin arzikin kasar.

Shugaban Amurka Barack Obama yace ya yi magana da shugaba Masar Hosni Mubarak,har ma ya yi kira gareshi da ya dauki “kwararan matakai” na cika alkawari da ya yi wa al’umar kasar cewa zai yi garambawul ga harkokin siyasar kasar.

Da yake magana da manema labarai a yammacin jiya jumma’a a fadar White, Mr.Obama yace ya yi magana da Mr.Mubarak dan shekaru 82 da haifuwa,jim kadan bayanda shugaban na Masar ya kammala jawabi ga al’umar kasarsa ta talabijin,wanda shine karo na farko day a magana tunda masu zanga zanga suka fantsama kan titunan kasar suna yunkurin hambare gwamnatinsa.

Haka kuma shugaban na Amurka ya bukaci gwamnatin Masar ta nisanci tarzoma kan masu zanga zanga cikin lumana,kuma ta maido da kafofin sadarwa da suka hada harda Internet da hukumomin kasar suka dakatar.

A cikin jawabinda ya gabatar,shugaba Mubarak ya yi alkawarin kaddamar canji a harkokin siyasa da tattalin arzikin kasar.Haka kuma ya rushe majalisar ministocin kasar, kuma ya yi alkawarin kafa sabuwar gwmanati yau Asabar.Yace kwanaki da aka dauka ana zanga zanga ba wani abu bane illa makarkashiyar ta tada zaune tsaye a Masar.

Har yanzu akwai gine gine da wuta ke ci a birnin alkahira, yayinda tankunan yaki na sojin kasar suke ci gaba da sintiri kan titunan birnin,fitar sojojin shine babban lamari,a lamari mafi muni a tarzomar da kasar ta fada,tun fara zanga zangar ranar Talata da ta shige.

Dubun dubatan masu zanga zanga ne suka yi biris da dokar hana yawo cikin dare suka ci gaba macin neman ganin Mr. Mubarak ya yi murabus, bayan ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar.

Jami’an kiwon lafiya sunce akalla mutane 13 ne aka kashe a birnin Suez a tarzomar da aka yi jiya jumma’a. Akwai rahotanni dake cewa fiyeda mutane 100 ne suka jikkata a duk fadin kasar baki daya.

‘Yan zanga zanga a birnin na Alkahira sun yi wa motocin jami’an tsaro zobe,a wani lokacin suka yi ta tura wata motar sulke ta soji a-yi-gaba-a-koma-baya, kamin su konata.Haka kuma masu zanga zanga sun yi kokarin kai wa tashar talabijin kasar hari.

An hangi wuta tana ci da karfi sosai a wurare daban daban cikin birnin,ciki harda sakatariyat ta jam’iyyar NDP mai mulkin kasar.Shaidu sun bada labarin jin kararrakin harbin bindiga.

Tun farko anan Washington,kakakin fadar White House Robert Gibbs, yace Amurka zata sake nazarin tallafin da take baiwa Masar wadda ya fi dala milyan dubu daya.

XS
SM
MD
LG