An Samu Karin Mace-Mace A Wani Hari Da Aka Kai A Sokoto

Wasu da ake zargin 'yan bindiga barayin Shanu a jihar Zamfara

An kashe mutane sama da 48 a harin da wasu masu bindigogi suka kai a kananan hukumomin da ke jihar Zamfara, Katsina da Jamhuriyar Nijer tsaka nin jiya da yau.

Kauyuka 4 ne lamarin ya shafa, da suka hada da Rakonni, Tsagi, da Kalhu da kuma Gi’ire, duk a cikin gundumar Gandi da ke karamar hukumar mulki Tarabah, inda ‘yan bindigar da ba’a gane adadinsu ba.

Masu bindigogin dai, sun fara kashe mutane 18 ne ranar Asabar da ta wuce, sai kuma jiya lokacin da a ke jana'izarsu, suka dawo suka sake bude wuta a kan jama'a, inda mutum 4 suka rasa ra'ikunsu.

Wakilin Muryar Amurka ya ce kananan hukumomin da ke Zamfara, sun dade suna cikin wannan al'amarin kai hari daga 'yan bindigan, kuma sun dauka abin ya lafa, amma sai kuma suka sake samun hari wanda har ya shafi sauran hukumomin da ke kusa da su.

Yanzu haka ana zaman dardar a garuruwa da dama a yankin gabashin jihar Sokoto saboda fargabar kai hari a kowane lokaci, yayin da wasu al’ummomi da dama suka bar garuruwansu.

Ga cikkaken rohoton wakilin Muryar Amurka Murtala Faruq Sayinna

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Karin Mace-Mace A Wani Hari Da Aka Kai A Sokoto 2'10"