An Yi Kashedi Ga Kamfanonin Sadarwa A Nijar Da Kada Su Yanke Internet

An gargadi kamfanonin wayar sadarwa a jamhuriyar Nijar, da kada su yanke wa jama'a damar amfani da yanar gizo a bisa dalilin da ba su ne su ka yi sanadi ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama da na kare masu saida kayan masarufi a jamhuriyar Nijar, sun gargadi kamfanonin sadarwa na wayoyi tare da yin kira ga gwamnatin kasar, da kada su zare wa mutane kudi ko data ta waya, ko da lokacin da suka dauka na kwanaki ko wata na anfani da data ta internet ya kare, kasancewar ba laifin su ba ne, na datse yanar gizon.

A daidai lokacin a ke cigaba da fuskantar yankewar yanar gizo a jamhuriyar Nijar, biyo bayan zanga-zanga da suka wakana a Yamai, babban birnin kasar don nuna rashin amincewa da sakamakon zabe zagaye na 2 na shugaban kasa.

Da yawan 'yan Nijar, sun soma kira ga gwamnati domin ta san cewa nauyi ya rataya a wuyarta, na biyan kamfanonin wayoyi diyya, don kuwa rashin bai wa jama'a damar samun yanar gizo, bayan sun biya kudinsu, ba abu ne da ya kamata a cire musu kudi ba, lokacin da aka diba na karewar intanet din mutane ya kamata a kara shi, tunda gwamnati ta sa aka katse yanar gizon.

Abdullahi Kado, shugaba na kasa a kungiyar kare hakkin bil'adama, 'yanci da walwala, ya ce, jama'ar kasar na cigaba da nuna bacin ransu game da wannan halin da a ke ciki, tare da kira ga kamfanonin waya da kar su yanke musu internet, koda sun kai wa'adin karewar layin nasu, tunda ba laifinsu ba ne ya sa a ka yanke, kuma ba su yi anfani da internet din ba a tsawon wannan lokacin.

Wannan lamarin na datse yanar gizo, ya sa masu anfani da ita don karatu, sana'a ko aiki, jikinsu ya mutu, kuma sun fada rayuwar duhu ta can shekarun baya, ba labarun halin da duniya take ciki.

Ga mai bukatar sauraron rahoton Harouna Mamane Bako cikin sauti, ga shi.

Your browser doesn’t support HTML5

An Ja Kunnen Kamfanonin Sadarwa A Nijar Da Kada Su Yanke Internet