An Yi Kira Ga Shugaba Joseph Kabila Ya Gudanar Da Zabe Na Gaskiya

Shugaba Joseph Kabila

Babban limamin darikar katolika a Demokaradiyyar Jamhuriyar Congo, ya yi kira da babbar murya da a gudanar da zaben 2018 cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba.

Limamin ya yi kira da a zauna lafiya yayin gudanar da zaben kasar Demokaradiyyar Jamhuriyar Congo, mai tattare da tsananin fargaba da tashin hankali, a wurin babban taron addu’a a jajibirin bukin Kirsimeti a babban birnin kasar Kinshasa.

A jawabin sabon babban limamin kirista a Kinshasa Archbishop Fridolin Ambongo, ya yi kira ga gwamnatin shugaba Joseph Kabila, da ta gudanar da zaben ranar 30 ga wannan watan na Disamba kamar yadda ta sanar a makon da ya gabata.

Ambongo, ya ce a daidai wannan lokaci mai muhimmanci ga tarihin kasar mu, ina jan hankali da tabbatar da hali na gari, kuma mu tabbatar da zabe cikin lumana, saboda mu kammala zaben na ranar 30 ga watan Disamba 2018 cikin kwanciyar hankali da gaskiya.

Darikar katolika a Congo ta dade tana bada goyon baya ga tsarin demokaradiyya ga kasar, kuma tayi ta kira ga Kabila ya gudanar da zabuka, wanda aka dage su tsawon shekaru biyu.