An yi Zaben Kananan Hukumomi a Jahar Yobe

Jami'an hukumar zaben Najeriya.

Sai dai an yi zaben kananan hukumomin ba tare da PDP ba wadda ita ce babbar jam'iyar hamayya a jahar Yobe
Kamar yadda gwamnatin jahar Yobe ta dage cewa sai an yi zabe, ba gudu, ba ja da baya, karshen ta dai an yi zaben kananan hukumomi a jahar asabar din nan, sai dai ba a samu cikowar masu kada kuri'a ba kamar yadda aka saba . Wannan ne karo na farko acikin shekaru biyar da aka yi zaben kananan hukumomi ba tare da jam'iyar PDP ba, wadda ita ce babbar jam'iyar hamayya a jahar Yobe. Kuma wannan ne karo na biyu da jam'iyar ta PDP ke kauracewa zabe a jahar Yobe. Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biu ya aiko da rahoto daga Damaturu babban birnin jahar Yobe:

Your browser doesn’t support HTML5

An yi zaben kananan hukumomi a Yobe - 1:37


Haruna Dauda Biu ya kara cewa al'amura sun tsaya cak a jahar ta Yobe sakamakon takaita zirga-zirgar ababen hawa domin a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.