Accessibility links

Yayin da ka soma mayarda hankali kan zaben 2015 wata sabuwar dambarwar siyasa ta soma kama wuta a jihar Kebbi

Wata sabuwar dambarwar siyasa na kokarin kunno kai a jihar Kebbi yayin da gwamnan jihar Saidu Usman Dakingari ke fuskantar adawa daga wasu na kusa da shi.

Wasu na hannun damansa ne suka fito karara suna kalubalantar tabarbarewar alamura karkashin shugabancin gwamnan da kuma kame bakinsa da ya yi kan cecekucen dake faruwa a jam'iyyarsa ta PDP. Yin hakan sun ce ya jefasu cikin rudu a siyasar jihar da ta kasar.

Alhaji Sani Dododo yana cikin hukumar alhazan jihar kuma yana daya daga cikin sanannun na hannun daman gwamnan shi ne ya yiwa 'yan jarida bayani kan matsayinsu. Ya ce alamarin siyasar jihar Kebbi ce ke da rudani da rashin sanin inda aka nufa. Ya ce babu abun dake tafiya a jihar daidai. Ya ce idan aka shigo garin Birnin Kebbi kamar inda aka yi yaki ya kare ne. Ya ce gwamna Saidu Dakingari ya kashe ma'aikatan jihar gaba daya. Aikin jihar ya lalace.Gwamnan ya kashe 'yan siyasar jihar ya kuma kashe 'yan kasuwa. Siyasar ma da ta kaishi kan kujerar shugabanci babu ita. Babu kuma wanda ya san inda aka nufa. 'Yan kasuwa na cikin masifa da tashin hankali. 'Yan siyasa kuma na cikin bakin ciki. Fatara da talauci da rashin abun yi sun yiwa mutane katutu. Ya ce sabuwa ko tsohuwar PDP suke ko kuma cikin wata jam'iyya daban domin basu san inda suke ba.Babu bayani babu magana da mutane kuma siyasa bata tafiya haka. Ya ce ya guji wadanda suke yi masa karya.

Amma shugaban PDP na jihar Kebbi Alhaji Mansur Shehu ya musanta zarge-zargen. Ya ce suna neman shugaban da zai dauki kudin jama'a su raba ma mutane su yi abun da suka ga dama shi ne cigaba a wurinsu. Ya ce ba'a diban kudi haka nan a rabawa jama'a. Ya kamata a yi anfani da kudi kan wasu shirye-shieye da zasu taimaki jama'a ba tare da an kauce ma ka'idar kashe kudin gwamnati ba. Idan batun kwangila ne bai yiwuwa a ce an ba kowa. Duk maganganun na 'yan adawa ne. Ya ce basu da wata banbancen siyasa. A jihar PDP daya suka sani.

XS
SM
MD
LG