An Zargi Hukumar Leken Asirin Sudan da Haddasa Wani Boren Sojoji

Harbe-harben bindigogi da aka ji jiya Talata a Khartoum babban birnin kasar Sudan, a lokacin da fada ya kaure tsakanin bangarori daban daban na rundunar sojojin kasar, sun bayyana raunin gwamnatin hadin gwiwar kasar.

Mai magana da yawun gwamnatin Faisal Mohamed Salih ya dora alhakin tashin hankalin a kan Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Kasar da ake kira NISS a takaice, wadda a baya ke goyon bayan tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, da aka hambarar da gwamnatinsa a wani juyin mulki da aka yi a watan Afrilun da ya gabata, bayan an shafe watanni ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar.

An mayar da hukumar ta NISS saniyar ware, tun bayan da aka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban, yayinda da sojojin Sudan da kuma wasu kungiyoyin mayaka da ake kira Rapid Support Forces da turanci suka zama kungiyoyin mayaka masu karfi na kasar.