Ana Cecekuce Kan Harkokin Kudi A Jihar Adamawa

Kofar shiga garin Mubi a Jihar Adamawa a bayan da aka kori 'yan Boko Haram daga cikin garin

Wani sabon rikici ya tashi a jihar Adamawa game da batun kudaden da gwamati ta karbo bashi daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi da kuma wadansu kudaden da aka ba gwamnan izinin kashewa ba tare da sawa a kasafin kudi ba.

Wannan batun dai ya kai ‘yan majalisar rusa kwamitin kudi da kuma dakatar da shugaban kwamitin daga zuwa majalisa har na tsawon watanni uku. Lamarin da ya kai ana zargin ‘yan majalisar da zama ‘yan amshin shata ta wajen amincewa da duk wani abinda gwamnan ya kawo gabansu a yanzu.

Sai dai kuma a wani taron manema labarai da ‘yan majalisar suka kira domin wanke kansu, sun musanta cewa sun zama ‘yan abi-yarima a sha kida. Inda shugaban kwamitin yada labarai na majalisar honorable Hassan Baruma ke cewa, an dakatar da shugaban ne domin an lura cewa ba zai rike kwamitin ba kuma yana maida majalisar tamkar gareji. Abinda yasa suka yi amfani da abinda dokar majalisar ta tanada suka dakatar da shi na tsawon watanni uku.

Dangane kuma da batun kudaden, Baruma yace sun yi shirin gudanar da bincike sai dai basu da cikakken bayanin abinda ke faruwa.

A nashi bangaren, shugaban kwamitin kudin yace, wannan ya tabbatar da abinda yake fada, ya kuma ce an zabesu ne bisa tunanin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi gaskiya, kuma ya kamata su yi koyi da shi.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul’aziz ya aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Kudi a Jihar Adamawa - 3'30"