Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Adamawa ta Amince Ta Biya Ma'aikata Hakokinsu


Jihar Adamawa

Bayan sun kwashi dan lokaci suna kai ruwa rana da kalamun dake tada jijiyar wuya tsakanin ma'aikata da jami'an gwamnati yanzu gwamnatin Adamawa ta amince ta biya ma'aikata daga tallafin da ta samu daga gwamnatin tarayya

Gwamnatin ta amince ta biya albashi da kudaden hutu da wasu alawus alawus.

Da yake bayyana matsayin da gwamnatinsa ta cimma gwamnan jihar Sanata Muhammad Bindo ya musanta zargin cewa gwamnatinsa na neman sauya akalan kudaden.

Ya godewa shugaban kasa Muhammad Buhari da ya fito da shirin tallafin domin jihohi su samu su biya albashi. Yace kodayake rance aka basu zasu biya amma ya taimaka kwarai. Abun da gwamnatin tarayya ta yi zai taimakawa ma'aikata da talakawa.

Tun farko dai jama'ar na ganin gwamnan nasu bai shirya karbar ragamar jan mulkin jihar ba. Irin wadanda ke fadan hakan gwamnan ya yi masu shagube.

Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Dauda Maina ya godewa gwamnan da ya kuduri biyan bashin da wasu suka bar masa ta handame kudaden da yakamata su biyasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

XS
SM
MD
LG