Ana Ci Gaba Da Shari'ar Wadanda Ake Zargin 'Yan Boko Haram Ne

Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktoba 2, 2014.

Ana ci gaba da shari'ar wasu 'yan Boko Haram su 1800 a Kainji da ke jihar Niger a Najeriya. Dalilin yin shari'ar a wurin shi ne jigilarsu zuwa Abuja zai yi wuya.

Hukumomin Najeriya an ci gaba da tuhumar wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne, wadanda yawansu ya kai 1800.

Mai gabatar da kara na gwamnatin Najeriya, Barrister Muhammad Umar Isu, ya ce shari'ar da ake yi wa wasu 'yan Boko Haram na tafiya kamar yadda aka tsara a garin Kainji da ke jihar Niger.

A ranar Litinin din da ta gabata kotu ta yanke hukumci akan wasu, haka kuma kotun ta yi ranar Talata yayin da ta daure mayakan Boko Haram 42.

Akwai wasu wadanda aka sallame su sboda ba'a same su da laifi ba.

Barrister Sunday Wujira da ya yi magana akan wadanda aka tsare shekara da shekaru amma aka sallame su saboda ba su yi laifin komi ba, ya ce tsarin dokokin kasar bai yi wani tanadin biyan diya ba ga wadanda aka rike shi ba,

Amma lauyan da ke kare hakkin bil Adama, Barrister Yakubu Saleh Bawa, ya yi tsokaci akan yadda ake gudanar da shari'ar a Kainji ba a baina jama'a ba.

A cewars, kundun tsarin mulki ya ce a yi wa mutum shari'ah ne a bayyane yadda kowa zai gani.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Ci Gaba Da Shari'ar Wadanda Ake Zargin 'Yan Boko Haram Ne- 2' 29"