Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekau Na Shigar Mata Don Badda Kama


Shekau a wani bidiyo da aka samu a watan Janairu.
Shekau a wani bidiyo da aka samu a watan Janairu.

Shugaban 'yan Boko Haram Abubakar Shekau na shigar Mata domin ya badda kama, amma sojojin Najeriya sunce sun sa masa tarko.

Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Burgediya Janar Sani Kukasheka ya bayyana cewa yakin da sojin ke yi da kungiyar Boko Haram karkashin shirin Operation Lafiya Dole na ci gaba da samun nasara.​

Domin ko yanzu haka rundunar tayi nasarar fatattakar ‘ya‘yan kungiyar daga inda suke da zama a cikin dajin Sambisa inda nan ne tungan su.

Baya ga korar ‘ya’yan kungiyar, rundunar ta samu nasarar kubutar da wasu mutanen da ‘yan kungiyar ta rike su har na tsawon wani lokaci mai tsawon gaske.

Sun kuma samu kayayyakin fada na kungiyar, da abubuwa hada boma-boma da suke anfani dasu a lokacin da suke kai hare-haren su.

Yayin da wasun su ke neman mafaka daga inda aka kore su wasu ko da kansu ne suka mika kansu da kansu ga jami'an sojan da ke yaki da su.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa daya daga cikin jagorar ‘yan Boko Haram wanda yayi kaurin suna wato Abubakar Shekau ya kasa jurewa wannan farmakin da sojojin ke kaiwa maboyarsu a cikin dajin na Sambisa.

Wannan ne yasa Shekau din yayi watsi da magoya bayansa don ya tsere.

Majiyar ta tabbatar cewa shugaban na ‘yan boko haram ya yi shigar mata, ta hanyar amfani da hijabi, kuma an ganshi cikin hijabin na mata mai kalar bulu da baki domin kokarin kaucewa daga sojojin da ke fatattakarsu.

Wannan ne yasa rundunar sojojin kira ga mabiyan nasa da su kwana da sanin cewa, suna biye ne da mutum mai raunin zuciya wanda ya gaza nuna cewa shi namiji ne saboda yaki fitowa fili ayi gaba da gaba da shi.

Har ila yau rundunar tayi kira ga sauran wadanda ke cikin dajin da su fito su mika kansu domin idan har aka kai musu hari kuma aka kama su to su yi kuka da kansu domin ba za ayi masu sassauci ba.

Rundunar tace tana nan tana iya bakin kokarinta na ganin ta danawa shugaban na Boko Haram tarko da za ta kai ga kamashi don haka ta bukaci jama'a da su mara masu baya musamman ma mutanen jihohin Adamawa, Borno da Yobe domin ganin an kawo karshensa.

Sojojin sun bukaci jama'ar wadannan jihohin da su sa ido ga Abubakar Shekau wanda zai iya badda kama cikin kayan mata musamman hijabi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG