Ana Fargabar Mutane Sun Mutu A Gidan Gwamnatin Sokoto

Wasu kafofi sun ce an yi hasarar rayuka da dama a lokacin, amma wasu majiyoyin sun ce raunuka kawai aka samu. Har yanzu babu wani abu daga bakin hukuma kan wannan lamarin.
Rahotanni dake iso mana cikin daren nan sun ce an samu mummunar turereniya a lokacin da ake raba wa jama'a kayan abinci na buda-baki a gidan gwamnatin Sokoto.