APC Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Rikicin Jihar Edo

Kwamitin aiyuka na jam'iyyar APC na kasa ya nada kwamiti domin samo bakin zaren magance rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakanin shugaban jam'iyyar APC da gwamnan sa na jihar Edo.

Sakataren Kwamitin Ahmed Aliyu Wadada ya yi bayani cewa za su yi tarurruka a jihar Edo, tare da masu ruwa da tsaki na jihar wanda ya kunshi jiga-jigai manya da matasa da mata, kuma an bawa kwamitin damar ba da laifi wa wanda ake ganin yayi laifi, san nan su kawo rahoton mafita da zai bada dama a yi demokradiya na cikin gida a jihar ta Edo.

Amma wasu fitattun shuwagabanin Jamiyyar APC, sun yi kira ga shugaban jam'iyyar Adam Oshimole da ya yi murabus daga kujerarsa, domin hakan zai kare jam'iyyar daga rushewa, wani abu da mai nazirin harkokin siyasar kasa da kasa Mohammed Ishaq Usman ke ganin shure shure baya hana mutuwa. inda yake ganin salon shugabancin da Oshimole ya kawo a jam'iyya shi ne irin na yakin kwato hakin ma'aikata a kungiyar kwadago ba wai shugabanci irin na siyasa ba.

Ganin cewa an jima ana rikice rikice a jihohin Ribas da lagos da Bauchi da Zamfara da Imo da Ondo da kuma Kaduna, amma ba a kafa irin wanan kwamiti ba, me ya sa APC ta farga ne yanzu?

Jigo a jam'iyyar APC Kanar Garus Gololo mai murabus, ya ce bai kamata wannan kwamiti ya tsaya a Jihar Edo kawai ba, ya kamata ya zagaya sauran jihohin kasar, inda ake samun baraka.

Abin jira a gani shine tasirin da wanan kwamiti zai yi wajen magance matsalar da ake samu a tsakanin shugabanin Jamiyyar APC a jihar ta Edo.