Azumi na kunno Kai Kayan Matsarufi na Kara Tsada

Wasu mata na sayen mangwaro a azumin shekarar da ta gabata.

Magidanta na kukan tsadar kayan matsarufi a lokacin da suka fara shirye-shiryen azumin dake tafe nan da 'yan kwanaki.

Allah Ya yi, shekara ta kawo mu, kwance tashi ga shi har za a fara azumin watan Ramalana, tuni har magidanta maza da mata sun fara zuwa kasuwanni domin saye kayayyakin fara azumin.

Kamar kowace shekara 'yan kasuwa sun fara tsawwala farashin kayayyakin matsarufi maimakon su yi rangwame albarkacin watan na Ramalana.

Daya daga cikin wakilan Sashen Hausa a garin Kaduna, Nasiru yakubu Birnin Yero ya zagaya kasuwannin garin domin ya ganewa idanun shi abubuwan da ke faruwa a wannan lokaci na sayayyar kayan fara azumi.

Your browser doesn’t support HTML5

Shirye-shiryen Fara Azumi a Najeriya - 2':58"

Baicin karin farashin kayayyakin abinci, hatta kayan sutura na sawa a jiki sun kara tsada inji daya daga cikin wadanda Nasiru Yakubu birnin Yero ya tattauna da su.