Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kalla Mutane 21 Suka Mutu Sandiyar Tashin Bom a Abuja


Tashin Bam Yau Laraba a Banex Plaza na Abuja.
Tashin Bam Yau Laraba a Banex Plaza na Abuja.

Yan sandan Najeriya sun ce mutane 21 a kalla aka kashe a cikin wata kakkarfar fashewar bom.

'Yan sandan Najeriya sun ce mutane 21 a kalla aka kashe a cikin wata kakkarfar fashewar bom da ta wakana a wata cibiyar hada-hadar kasuwanci a Abuja.

Kakakin 'yan sanda Frank Mba yace fashewar ta yau laraba a Emab Plaza ta raunata mutane 17 a kalla. Amma darektan hukumar ayyukan agajin gaggawa ta birnin tarayyar Abuja, Alhaji Abbas Garba Idris ya ce a nasu sanin mutane 52 ne suka raunata kuma su na samu kulawa a manyan asibitoci daban-daban a garin Abuja.

Babu bayani game da musababbin fashewar.

Wani shaida ya gayawa Muryar Amurka cewa wani bom din da aka dasa a cikin wata mota ne yayi bindiga. Amma wasu kuma sun ce wani mutum ne akan babur ya wurga wani bom.

Wakiliyar Muryar Amurka a Abuja Heather Murdock ta je inda bom din ya fashe, ta ce wurin ya na hargitse.

XS
SM
MD
LG