Ba'a Kashe Kowa a Saudiyya Ba Inji Jakadan Najeriya

Sarkin Saudiyya Salaman

An sami hatsaniya tsakanin baki da hukumomin kasar Saudiyya game da kamen ‘yan share wuri zauna ba tare da bin ka’ida ba.

A makon da ya gabata ne dai aka sami labarin yadda ake fatattakar ‘yan Afrika daga kasar Saudi din ciki har da ‘yan Najeriya. Har da jitajitar cewa ma wasu sun rasa rayukansu a wannan wasan buya tsakanin baki da jami’an tsaron kasar. To amma jakadan najeriya a kasar Abubakar Bunu y ace kawai shaci fadi ne maganar rayuka da aka ce an rasa.

Ya jaddada cewa ba ‘yan Najeriya kawai ake kora ba harda ‘yan wasu kasashen, musamman ma ‘yan Nijar, Habasha da wasu ‘yan Afrikan. Karshe yayi kira ga duk wanda ke da matsalar takardun zaman Saudi to su yi kokari su gyara in har suna son zaman kasar.

Dan majalisa Ibrahim Bello Rigachikun daga Kaduna yayi kukan yadda ake wa ‘yan Najeriya a Afrika ta Kudu amma yace na Saudiyya gangancin mutanen Najeriya ne da ke zuwa daga Umra su fake har sai sun yi aikin hajji maimakon su bi ka’idar yadda ake yi.

Hukumar Alhazan Najeriya ta bakin Abdullahi Mukhtar sun kwabi masu jigilar mutane zuwa Saudi to su yi hattara sannan duk wanda aka gane yayi jigilar irin wadannan mutane to ya kashe kamfaninsa. Ya ce yanzu da wuri ake gane bakon haure saboda maganar bullo da fasfon tafiye-tafiye mai aiki da na’ura mai kwakwalwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba'a Kashe Kowa a Saudiyya Inji Jakadan Najeriya - 3'50"