Ba Ma Nuna Banbanci Wajen Gudanar Da Ayyukanmu - Magu

Ibrahim Magu Shugaban Hukumar EFCC

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, Ibrahim Magu, ya sha nanata cewa hukumar ba ta nuna bambancin siyasa ko wani dalili wajen kama wadanda ta ke tuhuma da zarmiya.

Irin wannan zargi kan taso ne a duk lokacin da hukumar ta kama wani wanda a ke ganin ba ya jam'iyyar APC mai mulki ko ba ya shiri da gwamnatin Buhari.

Sanata Shehu Sani

A baya-bayan nan hukumar ta kama Sanata Shehu Sani wanda tun ficewarsa daga APC gabannin babban zabe ake zargin yana sukar lamirin manufofin gwamnatin.

A bitar ayyukansa na shekara, shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu ya fadi yadda yake fatar tarihi zai tuna da shi.

Shugaba Buhari ya ci gaba da alwashin yaki da barayin biro a duk lokacin da ya samu damar yin bayani.

EFCC

Saurari cikakken rahoto cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Ma Nuna Banbanci Wajen Gudanar Da Ayyukanmu - Magu