Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Ya Kira Taron Manyan Kwamandojin Kasar

Taron rundunar sojoji

A Wani matakin kara tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janaral Farouk Yahaya na can na gudanar da wani gagarumin taro da baki dayan manyan kwamandojin rundunonin sojin kasar.

Da yake bude taron, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janaral Farouk Yahaya ya ce za su yi duk wani abu mai yiwuwa wajen kare 'yanci da diyancin Najeriya ta yadda ba za su bari kasar ta ruguje ba.

Taron rundunar sojoji

Taron wanda ya tattaro baki dayan manyan kwamandojin rundunonin sojin kasar na da zimmar bitar inda aka fito da inda ake da kuma inda aka nufa, ma'ana za a duba irin na tsanaki dangane da irin ci gaban da aka samu da tangardar da aka fuskanta da nufin tsara yadda za a tukari sha'anin tsaro a cikin kasar.

Laftanar Janaral Yahaya ya ce ba ko tantama bisa irin rawar gani da aka cimma, kai-tsaye a iya cewa lalle kwalliya na biyan kudin sabulu musamman ganin har yabo dakarun kasar suka samu daga cibiyar nan dake sa ido kan ta'addanci a duniya wato Global Terrorism Index dangane da yadda aka cimma gagarumar nasara wajen yaki da 'yan ta'adda.

Rundunar sojoji

Bugu da kari, Janar Yahaya ya ce an kuma yi rawar gani wajen dakile 'yan bindigar arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da kuma masu fafutikar raba Najeriya a shiyyar kudu maso gabashin Njeriya,

Babban Hafsan hafsoshin ya sha alwashin kara jan damara wajen ganin dakarun kasar cikin aiki tare da sauran jami'an tsaro sun yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da samar da cikakken tsaro a duk sassan kasar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Hafsan Hafsoshin Sojoji Ya Gudanar Da Wani Gagarumin Taron Tsaron Manyan Kwamandojin Sojin Najeriya