Babban Jami'in Amurka Ya Kai Ziyara Ukraine

Mai baiwa fadar White House shawara kan harkokin tsaro, John Bolton ya isa birnin Kyiv –ziyararsa ta farko da wani babban jami’in Amurka ya kai kasar Ukraine tun bayan zaben Shugaba Volodymyr Zelenskiy a watan Afrilu.

“Jakada Bolton ya zo nan ne don nuna goyon bayan Amurka ga Ukraine, da yankinta da kuma dangantakarta da kasashen Turai. Ya na sa ran yin tattaunawa mai ma’ana da jami’an Ukraine,” a cewar wani sakon Twitter da ofishin jakadancin Amurka a Kyiv ya kafe yau Talata.

Kwana daya kafin wannan ziyara, Bolton ya aika da sakon Twitter dake cewa Amurka na goyan bayan 'yunkurin Zelenskiy wajen samar da sauyi da kuma kafa hanyar da za ta kai da ci gaban Ukraine,” duk da fadan da ake ci gaba da yi tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan awaren da Rasha ta ke mara wa baya a gabashin kasar.