Babbar Kotun Tarayya Ta Bayar Da Umarnin Sakin Zakzaky Da Bashi Diyya

Sheikh Zakzaky

Babban kotun tarayyar Najeriya ta bayar da hukuncin a saki Mallam Ibrahim El-Zakzaky cikin kwanaki 45, a kuma bashi diyyar Naira Miliyan 50.

Hukuncin umarnin sakin Ibrahim El-Zakzaky ya zone kimanin shekara daya bayan tsare shi da jami’an Najeriya suka yi, biyo bayan arangamar ‘yan kungiyar Shi’a da sojoji a Zaria da hakan ya haddasa asarar rayuka.

Mai shari’a na babbar kotun tarayya Alkali Gabriel Kolawole shine ya bayar da umarnin, bayan ga sakin nasa cikin kwanaki 45, a kuma bashi diyyar Naira Miliyan 50 da kuma gina masa sabon gida a duk inda ya zaba a jahar Kaduna.

Daya daga cikin lauyoyin El-Zakzaky Haruna Magashi, wanda kuma yayi murna da hukuncin yace zabin mallam ne kamar yadda kotu ta bayyana dan gane da inda yakeso ya zauna a gina masa gida.

Shi kuma lauyan hukumar jami’an tsaron asiri DSS Tijjani Gazali, yace zasu nazarci hukuncin don daukar mataki na gaba.

Mai shari’a Gabriel Kolawale dai a hukuncin na sa mai shafi 50 yace babu korafi daga makwabtan El-Zakzaky cewa yana muzguna musu a Zaria. Cikin rahotan kwamitin Shari’a na gwamnatin jahar Kaduna, ya samu jami’an El-Zakzaky da takurawa al’ummar Gillesu a Zaria inda yake gabanin akasin.

Domin Karin Bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Mallam Ibrahim El-Zakzaky Ya Samu Nasarar Hukuncin Kotu - 2'43"