Batu Tabbas A Cimma Burin Sake Obamacare

Shugaban masu rinjaye a majalisar datijan Amurka Mitch McConnell

Har yanzu da saura rina a kaba a yunkurin 'yan jam'iyar Republican na soke tsarin inshorar Amurka da ake kira Obamacare

Sa’oi a bayan da 'yan majalisar dattijai na jam’iyar Republican suka kada kuri’ar fara muhawara kan yunkurin soke dokar fitaccen tsarin kula da lafiya na tsohon shugaban kasa Barack Obama, majalisar ta kasa amincewa da wani kuduri da zai bada damar cimma wannan gurin.

Jiya talata ‘yan majalisar suka kada kuria inda arba’in da uku suka goyi baya hamsin da bakwai kuma suka ki amincewa da kudurin da shugaban masu rinjaye Mitch McConnell ya gabatar na kawo karshen fadada tallafin kiwon lafiya da ake ba marasa galihu, da zabtare tallafin da ake ba masu karamin karfi domin biya kudin inshora na kashin kansu, da kuma kawar da harajin da ake yiwa wadanda basu sayi inshorar kula da lafiyarsu ba.

Matakin ya kuma hada da gyaran da dan jam’iyar Republican mai wakiltar jihar Texas Ted Cruz ya yi da zai sa kamfanonin inshora su samar da damar kula da lafiya da bai kai wadda ke karkashin tsarin inshora na Obamacare ba.

Kuri’ar da aka kada jiya talata da dare, tana cikin jerin kuri’u da za a kada a cikin wannan makon, a yunkurin jam’iyar Republican na sokewa da kuma maye gurbin tsarin inshorar da aka fi sani da Obamacare. Majalisar dattijai zata fara muhawara ne bayan yunkurin McConnell sau biyu a lokutan baya basu cimma nasara ba. Ko a wannan lokacin ma, kadan ya rage ya sake gamuwa da cikas, bayanda dukan ‘yan jam’iyar Democrat da kuma ‘yan jam’iyar Republican guda biyu suka ki amincewa, abinda ya sa aka yi kunnen doki a zauren, da kuri’u hamsin hamsin.

Sai da mataimakin shugaban kasa Mike Pence a matsayinsa na shugaban majalisar dattijai, ya kada kuri’ar raba gardama.

Dan jam’iyar Republican mai wakiltar jihar Arizona John McCain ya kada kuriar da kawo karshen ja in ja, wanda ya dawo majalisa ‘yan kwanaki kalilan bayan da aka gano yana da cutar sankarar kwakwalwa.