Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam'iyyar Republican Na Shirin Sake Wa ObamaCre Kwaskawrima


'Yan Jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawa na shirin sake wani yinkuri a wannan satin, game da aniyarsu ta sake dokar kiwon lafiya da tsohon Shugaba Barack Obama ya kafa.

Majalisar Dattawan Amurka, ta gwada wasu kudurorin dokar kiwon lafiya biyu, wajen neman yadda za ta iya maye gurbin ta yanzu da aka fi sani da Obamacare da kuma wacce za ta maye ta sannu a hankali cikin tsawon shekaru biyu saboda 'yan Majalisar su samu lokacin yin cikakken nazarin yadda za a maye gurbin ta yanzun.

Dukkannin kudurorin dokar sun gamu da adawa daga 'yan Democrats da kuma wasu 'yan Repulican ta yadda babu kudurin da ya yi nisa a yinkurin maida shi doka.

Sanata John Thune, daya daga cikin 'yan Republican 52 a majalisar mai kujeru 100, ya fadi jiya Lahadi cewa Shugaban Masu Rinjaye Mitch McConnel zai bude babin kuri'ar cigaba da muhawara kan daya daga cikin kudurorin da kuma duk wata kwaskwarimar da ake bukata.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG