Bamu Yi Fushi Da Hanamu Shiga Wadansu Wurare Ba A Borno-Dr Hakeem Baba Ahmed

BORNO: Ziyarar kwamitin sa ido na Majalisar Dattawa akan harkokin IDPs

Kungiyar dattawa Arewacin Najeriya karkashin jagorancin Alhaji Maitama Sule, ta kai ziyarar gani da ido jihar Borno, da nufin jajintawa da kuma nuna goyon baya ga al’ummar jihar.

A cikin jawabinsa, tsohon jakaden Najeiyan na dindiindin a Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana cewa, duk da yake an fara samun zaman lafiya, amma sun san akwai jan aiki a gaba na sake tsugunar da wdanda abin ya shafa, ya kuma ce lamarin ya shafi Arewacin Najeriya ne baki daya.

Sai daiirundunar sojan Najeriya ta gurguntar da yunkurinsa kungiyar dattawan bayan kwana daya a garin Maiduguri, na ziyartar wadansu wuraren cikin jihar da suka hada da sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori, domin ganewa idonsu halin da al’ummar jihar ke ciki.

Da yake maida martani dangane da wannan matakin, daya daga cikin dattawan da suka kai ziyarar, Dr Hakim Baba Ahmed yace basu yi fushi da jami’an tsaron ba, kasancewa akwai ka’idoji, mai yiwuwa wadanda ya kamata su sanar dasu game da ziyarar kungiyar dattawan basu yi haka ba. Yace, wannan bata zama matsala ba. Bisa ga cewarshi, kungiyar zata sake shiri ta dawo, tana kuma fatar lokacin da ta dawo ba zata sami mutanen a halin da suke ciki yanzu ba.

Dr Hakeem Baba ya kuma yaba kokarin da rundunar tsaron kasar ke yi na shawo kan wannan lamarin, ya kuma godewa dukan wadanda suke bada gudummuwa a wannan fafatuka.

Your browser doesn’t support HTML5

Ziyarar dattawan arewacin Najeriya jihar Borno-3:36

Tun farko a jawabinsa, gwamnan jihar Borno Kashim Shatima ya godewa kungiyar dattawan arewacin Najeriyan domin karamci da kuma goyon bayan da suke ba jihar tunda ta fara fuskantar kalubalatar tsaro.

Ga cikkaken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga Maiduguri, Jihar Borno,