Ban Ki-moon Ya Yi Tur da Hari Kan Wani Asibiti dake Yamal

Ban Ki-moon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Kamar yadda ya faru a Afghanisatan harin da jiragen sama ke kaiwa kan Yamal a karkashin jagoranci Saudiya ya fada akan wani asibitin jin kai

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi tir da harin saman da ya fada kan asibiti a kasar Yamal, inda yace asibitoci da ma’aikatansu suna da kariya a karkashin dokokin ayyukan jin kai.

Ya kuma bukaci a gudanar da binciken gaggawa don gano inda matsalar take ba tare da son kai ba, wanda abin ya faru ne a arewacin yankin Saana ta Yamal.

Kungiyar jin kai ta Likitocin nan Doctors Without Borders ta fada a jiya Talata cewa harin sama na sojojin da Saudiya ke jagoranta ne ya fadawa asibitin, amma ba a sami mummunar jikkata ba.

Daraktan kungiyar a Yamal din Hassan Boucenine ya kushe wa gamayyar sojojin masu kai hare-haren da jiragen saman yaki. Yace kwanan nan sai da Doctors Without Borders suka baiwa gamayyar sojojin taron dangin taswirar da zata nuna daidai inda asibitin yake.