Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-moon Ya Gargadi Yahudawa da Falasdinawa Su Kawo Karshen Rikicinsu


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayinda yake jawabi jiya a Israila

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi gargadi game da amfani da karfin soja a rikicin Isra’ila da Falasdinawa

Yayi wannan gargadin ne a lokacin ganawarsa da Firayiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a kokarin kwantar da tarzomar kusan makonni uku.

Mista Ban ya kuma ja kunnuwan Israila da Falasdinawa su gujewa hatsarin yaduwar rikicin a addinance da irin illar da hakan zai yiwa yankunan kasashen. Ya kuma yi kira da ayi duk iyakar abun da zai yiwuwa don ganin hakan bata faru ba.

Sakataren ya fadawa manema labarai cewa, yunkurin jami’an tsaron Israila yana iya samun tirjiya, in har basu yi kokarin kashe wutar rikicin kafin mutane su rasa rayukansu ba.

A daya bangaren kuma, a Larabar nan ce ake sa ran Sakataren Wajen Amurka John Kerry zai tashi zuwa Turai da Gabas ta Tsakiya bisa yunkurin taimakawa wajen kashe wutar rikicin Yahudawa da Falasdinawa akalla 50 ne suka hallaka a rikicin.

Sannan zai tuntubi kawayen Amurka a game da maganar tsaro da ya hada da barazanar ISIS da kuma rikicin Syria da Ukraine. Ana sa ran zai gana da takwarorinsa na Saudiyya, Turkiyya, Rasha da Jordan.

Amma karfin ziyarar shine ganawa da Benjamin Netanyahun Isra'ila da Mahmoud Abbas na Falasdinu.

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG