Bangaren Kamaru dake Turanci Yana Korafin An Maidashi Saniyar Ware

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Bangaren dake turanci a kasar Kamaru ya kwashe watanni biyu yana fafatawa da gwamnatin kasar, amma ya dakatar domin ya saurari jawabin shugaban kasar na karshen shekara kafin daukan mataki na gaba.

Shugaba Paul Biya a cikin jawabinsa na karshen shekara yace Kamaru kasa daya ce kuma ba zasu taba yadda da tashin hankali a cikin kasar ba, inji shugaban.

Shugaban yace idan har wasu mutane suna bukatan a biya masu muradunsu to dole ne su kawo muradun a kan teburin shawara. Sai dai yace abun da ya faru a birnin Bamunga suna bin lamarin kuma duk wanda aka samu yana da hannu a cikin rikicin zai dandana kudarsa.

Wani dan birnin Bamunga wanda jigo ne a kungiyarsu ta masu turanci da ya nemi a sakaya sunansa yace maganar da shugaban kasa yayi bata dace da bukatunsu ba saboda ba abun da suke jira ba ke nan. Yace dama sun tsayar da zanga-zangar da suka fara su ji abun da zai ce kana uku ga wannan watan su yanke shawarar daukan mataki na gaba. Yace duk abun da ya kamata su rubuta masa sun yi amma bai basu amsa ba.

Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Bangaren Kamaru dake Anfani da Harshen Turanci Yana Korafin An Maidashi Saniyar Ware - 3' 21"