Bankin Duniya Ya Tallafawa Yankin Da Aka Yi Ambaliyar Ruwa A Naija

Barnar Da Ambaliyar Ruwa Yayi A Jihohin Adamawa Da Taraba

Bankin Duniya ya bayar da tallafin kudi, dalar Amurka Miliyan biyu domin fara aikin gyara wuraren da zaizayar kasa ta shafa sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta bana a jihar Neja dake Arewacin Nigeria.

Shugaban Shirin kula da wuraren da zaizayar kasa ta yima illa dake karkashin Ma’aikatar Muhallin Nigeria Alhaji Salisu Dahiru yace ko baya ga wannan Bankin duniyar yayi Alkawalin bayar da Karin kudi idan akwai bukata domin ganin an kamala aikin da yace an riga an fara.

Alhaji Salisu Dahiru yana magana ne a lokacin ziyarar da suka kaiwa Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello a Minna domin bayyana mashi halin da ake ciki akan fara wannan aiki.

Gwamna Abubakar Sani Bello dai yace gwamnatin jihar ta damu matuka akan wannan matsala sabili da haka gwamnatin jihar take kokari domin kai dauki a wuraren da aka samu wannan matsala.

Gwaman yace yanzu haka sun bayar da Naira Miliyan 200 daga cikin Naira Miliyan 500 da zasu kashe akan matsalar zaizayar kasar a jihar. garin Rafin Gora yafi ko’ina fuskantar matsala saboda haka yana bukatar daukar matakin gaggawa kuma yana bukatar gwamnatin tarayya ta kara baiwa garin kulawa ta musamman.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari

Your browser doesn’t support HTML5

Bankin Duniya ya bada tallafi a Naija-2:43"


Bankin