Barcelona Ta Yi Wa Nyemar Tayin Kwangilar Euro Miliyan 190

Jami’an kungiyar PSG na Qatari, sun nuna rashin jin dadi da halayyar Neymar a wannan bazarar kuma suna shirin su sake shi ya tafi.

Barcelona ta yi wa dan kwallon kafa Nyemar tayin kwangilar Euro miliyan 190 don ya buga wa kungiyar Paris Saint-Germain, a cewar wani rahoto na ESPN.

Sai dai an fahimci cewa PSG ta yi watsi da tayin, wanda da zai sa Neymar ya koma Camp din na Nou amma a matsayin aro.

Barca ta yi tayin ba da kudi sama da € 40m kudi amma na aro, a bisa tanadin cewa zata bada karin euro miliyan 150 don rattaba hannu kan wannan dan kwallon, dan assalin Brazil na zama dan wasanta na dindindin a bazara mai zuwa.

Jami’an kungiyar PSG na Qatari, sun nuna rashin jin dadi da halayyar Neymar a wannan bazarar kuma suna shirin su sake shi ya tafi.

Amma hukumomin gasar Lig na farko za su amince da matakin ne kawai idan har zasu iya maido da kudinsu kusan adadin € 222 miliyan da suka kashe wajen kawo shi Paris daga Barcelona a shekarar 2017.

Sun kuma yi imanin cewa Barcelona ba za ta iya biyan kudin musayar duka a lokaci daya ba a bazara mai zuwa, idan har suka mai da wannan zamansa a cikin kungiyar na dindindin, don haka za su nemi su rinka biyan shi a shekara-shekara, wanda hakan ba zai dace da tsare-tsaren kungiyar ta Faransa ba.