Bauchi: Mutane Sama Da 30 Sun Rasa Rayukansu Bayan Da Kwale Kwalensu Ya Kife

Hadarin Kwale Kwale Jihar Kirfi

A Najeriya rahotanni daga jihar Bauchi na hadarin jirgin daya faru a karamar hukumar Kirfi, na nuni da cewa ana kyautata zaton mutane sama da 30 ne suka mutu, kokuma sun bace a sanadiyar kifewar jirgin ruwa da yake dauke da mutanen kauyukan dake yankin karamar hukumar wanda yawancinsu manoma ne.

Wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad ya tattauna da dan Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Abdulkadir Umar Dewu dake garin Kirfi domin bin diddigin lamarin, sai dai ya ce basu da masaniyar yawan mutanen da ke cikin kwale kwalen, an kuma kamanta yawan wadanda suka mutu 30, amma ba a tabbabtar ba.

Ya kara da cewa, har ya zuwa wannan rahoto jama'a na ta zuwa neman 'yan uwansu da suka shiga wannan kwale kwale.

Ya bada shawarar cewa dole gwmanatin tarayya to shigo don ta taimaka wa karamar hukumar Game da wannan matsala, a kuma samo masu sauki. Ya ce wadanda suka iya ruwa a jikin su, sun fito da rai, amma dayawa sun rasa rayukansu.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

Bauchi: Mutane 30 Suka Rasa Rayukansu A Hatsarin Kwale Kwale