Bawumia: Matasan Ghana Kada Ku Bari 'Yan Siyasa Suyi Amfani Da Ku

Mataimakin shugaban kasar Ghana Alhaji Mahamud Bawumia, ya halarci bukin Maulidin haihuwar fiyayen halitta Annabi Muhammad, wanda Shiekh Abdul Wadud Haruna yake shiryawa duk shekara.

A cikin jawabinsa mataimakin shugaban kasan Bawumia yace matasa, musanman a cikin unguwanin Zango kar su yadda ana amfani dasu cikin harkokin da suka kauce hanyar Allah, har su tsunduma rayukan su cikin hadari.

Mataimakin shugaban kasa Bawunia yayi wa matasa dake yadda ana amfani dasu wurin tada zaune tsaye hanun ka mai sanda, yana mai fadan cewar shugaba Akufo Addo, ya bayyana aniyansa na tabatar da ganin bayan harkokin 'yan bangan siyasa ko da kuwa ana ha maza, ha mata.

Sai ya kara da cewar matasan kasar, kada su bari ayi anfani dasu wajen aikata ayyuka da zasu zama barazana ga rayuwar su. Shugaba Akufo Addo ya tsai da matsayar kawo karshen harkokin 'yan bangan siyasa, kuma ya sha nanata aniyar sa ta tsayawa daram dakau akan taimakama matasa.

Bukin maulidin ya samu halartan mashahuran malamai daga ko ina cikin Afrika, kamar Najeriya, Nijar, Senegal da sauransu. Ga rahoton Ridwan lah Muktar Abbas daga Accra Ghana.

Your browser doesn’t support HTML5

Bawumia: Matasan Ghana Kada Ku Bari 'Yan Siyasa Suyi Amfani Da Ku 2'10"