Binciken Cibiyar IBP Ya Gano Abubuwa Masu Kawo Cikas Ga Yaki Da Annobar COVID-19 A Duniya

Wani rahoton cibiyar bincike ta International Budget Partenership ya gano rashin haske wajen tafiyar da kudaden da aka yi tanadi domin yaki da anobar COVID-19a kasashe da dama

Yayinda a wani bangare abin ya haifar da take dokoki da ka’idodin aiki a fannoni da dama saboda haka cibiyar ta gargadi gwamnatoci su gyara irin wadannan kura-kurai dake dabaibaye yunkurin murkushe wannan bala’ai da ya addabi duniya.

Rahoton wanda aka baje a wata mahajar bainar jama’a wacce kungiyar AEC ta shirya ya biyo bayan wani binciken da cibiyar IBP ta shafe watanni da dama tana gudanarwa a kasashe kimanin 120 da nufin tantance zahirin yanayin tafiyar yaki da cutar coronavirus daga farkon bullar annobar zuwa yanzu.

Kimanin biliyon 14 na dalar Amurka ne aka bayyana cewa an ware a matsayin kashi na farko na kudaden zartar da matakan yaki da cutar a duniya, to sai dai wannan bincike ya gano rashin haske a game da yadda aka kasafa wadanan kudade a kasashe da dama.

Wani dan rajin kare hakkin dan adam Diori Ibrahim da ya halarci wannan mahawara ya ce bai yi mamakin jin bayanan da binciken na IBP ya bankodo ba saboda yadda jami’ai a kasashe da dama na nahiyar Afrika suka maida rubda ciki da dukiyar jama’a tamkar sana’a.

Yaki da annobar COVID-19 wani abu da ya haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin hukumomi da talakawa a kasashe da dama inda matakin kulle da takaita harkoki suka janyo tarzoma kamar yadda a yanzu haka batun allurar rigakafi ke ci gaba da haddasa mahawara inda hatta a kasashen da suka ci gaba ake samun masu danne matakan da aka shimfida da zummar dakile yaduwar wannan masifa da ta addabi duniya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Binciken Cibiyar IBP Ya Gano Abubuwa Masu Kawo Cikas Ga Yaki Da Annobar COVID-19 A Duniya