Birtaniya Tayi Alkawarin Biliyan $1.6 Domin Yaki Da Kanjamau, Tarin Fuka Da Cizon Sauro

PM kasar Britaniya David Cameron

Kasar Birtaniya zata bada dala biliyan 1.6 ga gidauniyar kudin kasa ta duniya domin yaki da kanjamau, tarin fuka da cutar cizon sauro a cikin shekaru uku masu zuwa da fatar shawo kan cutukan da suke kisa.

Ministan harkokin tallafawa kasashen ketare na Birtaniya Justine Greening yace gwamnatin Birtaniya zata bada fam biliyoyin daya ko kuma fan miliyan 333 (miliyan $533.9) a shekara, a cikin 2014-2016 na tara kudin. Mr. Greening ya bayyana haka ne a wajen taron gidauniyar da aka yi a birnin Geneva

A farkon wannan watan gidauniyar tace tana bukatar dala biliyan 15 a cikin shekara uku masu zuwa domin yaki da wadannan cututtukan.

Banda Birtaniya, Amurka ma ta kebe kudi a kasafin kudinta na 2014 omin yaki da cututukan.

Babban taimako yana zuwa ne daga gwamnatocin kasashen OECD. Ana kuma samun taimako daga kungiyoyi masu zaman kansu kamar gidauniyar Bill da Melinda Gates da kuma Koka-Kola.