Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tace An Sami Ci gaba A Yaki Kan Kanjamau


UNICEF

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, an sam raguwar masu mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kanjamau sakamakon karin magunguna da ake samu.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, an sam raguwar masu mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kanjamau sakamakon karin magunguna da ake samu.

A cikin rahoton, an bayyana cewa, kimanin mutane miliyan talatin da biyar da dubu dari uku ne a duniya suke dauke da cutar a halin yanzu. Cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya, UNAIDS tace yawan mutuwa daga kanjamau da HIV suna raguwa, kuma yawan mutane masu samun lafiya na karuwa.

Mutuwa irin ta kanjamau a 2012 ta ragu zuwa Miliyan daya da dubu dari shida daga miliyan daya da dubu dari bakwai a sheakara ta 2011 da kuma sama da miliyan biyu a shekara ta dubu biyu da dari biyar. Kuma yawan mutanen da suke kamuwa da cutar ya ragu zuwa miliyan biyu da dubu dari uku a shekara ta 2012 daga miliyan dubu biyu da dari biyar a shekara ta 2011.

Tun 2001, ruhoton Majalisar Dinkin Duniya yace, an sami kimanin raguwar kashi 52 na kamuwar HIV cikin yara da kuma kashi 33 sabbi cikin manya da yara.

Wannan ruhoton na UNAIDS ya nuna cewa duk da kokarin masu bayarwa domin cigaban wannan aiki na HIV, kashewar kudi ta kasashe masu wannan cutar tana karuwa, wanda yakai ga kashi 53 na dukan kashe kudade kan HIV a 2012.

Kwayar cutar HIV wadda ke kawo cutar Kanjamau tana yaduwa ta wurin bada jini, shan mama da kuma ta wurin jima’i, amma za’a iya lura da shi tawurin amfani da magunguna.

Dukan kudaden da aka tara domin yaki da cutar kanjamau a 2012 shine biliyan $18.9, kimanin biliyan $3 zuwa biliyan $5 kasan kudin da aka kiyasta na biliyan $22 zuwa biliyan $24 da ake bukata kowacce shekara zuwa 2015.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG