Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kungiyoyi Sun Hada Hannu a Yaki Da Cutar Kanjamau


HIV AIDS
HIV AIDS

A kokarinta na kawar da cutar kanjamau, gwamnatin kasar Amurka ta sake bayyana shirinta na hada kai da kungiyoyi da gwamnatoci karkashin shirin shugaban kasa na gaggawa domin kawar da kanjamau

A kokarinta na kawar da cutar kanjamau, gwamnatin kasar Amurka ta sake bayyana shirinta na hada kai da kungiyoyi da gwamnatoci karkashin shirin shugaban kasa na gaggawa domin kawar da kanjamau.

An bayyana haka ne a wajen wanin taron manyan kungiyoyin da kuma wakilan shugabannin kiyaye kanjamau da aka yi a jihar Legos.

Wakilan Amurka a wajen taron sun kuma ziyarci wani asibiti dake tsibirin jihar Legos domin su ga kokarin da ake yi na kawarda yaduwar wannan kwayar cutar, da kuma manufar cinma burin hana yaduwar cutar baki daya da kuma shawo kan nunawa masu fama da cutar banbanci. Haka kuma ana kokarin ganin cutar ta daina kashe mutane baki daya.

Bukin ya sami hallatar masanan magani, da masu maganin gargajiya masu aiki tsakanin mutane dake dauke da kwayar cutar.

Shugaban wakilan cibiyoyin Amurka USAID/PEPFAR, Mr. David Stanton, ya kara bayyana bukatar daukar matakin hana yada cutar daga uwa zuwa jariri, yace wannan ita ce muhimmiyar hanyar maganin yada cutar. Ya kuma tabbatarwa kungiyoyin cigaban hadin kan mutanen Amurka na yaki da kwayar cutar.

PEPFAR wata kungiya ce da ta bada tallafin dalai biliyan goma sha biyar domin yaki da cutar kanjamau na tsawon shekaru biyar daga 2003 zuwa 2008 karkashin tsohon shugaban Amurka, George W. Bush, domin yakin da cutar kanjamau.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG