Paul Biya Zai Sake Shiga Takara

Paul Biya- shugaban kasar Kamaru

Dadadden shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya sanar da zai sake shiga takarar shugabancin kasar na wani sabon wa’adi.

Biya, ya dare a kan shugabancin Kamaru tun shekarar 1982 kuma shine shugaban kasa na biyu da yafi dadewa a kan karagar mulki a nahiyar Afrika, bayan shugaban Equitorial Guinea, Teodoro Obiang.


A shekarar 2008 ne Biya ya soke adadin wa’adin shugabanci kasar, lamarin da ya bashi damar ci gaba da shiga takara kuma ya lashe zaben shekarar 2011.


Kasar Kamaru tana fama da hare-haren Boko Haram a arewacin kasar da kuma kungiyar yan awaren kasar, a yankuna biyu na masu amfani da harshen Ingilishi.