Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya Ta Saki Mutane 593

Wasu 'yan Boko Haram da suka mika kansu da kansu a shekarun bayan

Rundunar sojan Najeriya ta Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri ta mika wasu mutane da ta wanke su 593 da aka kame lokaci da ake yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram ga gwamnatin jihar Borno.

Rundunar ta saki mutanen ne wadanda mafi yawansu mata ne da kananan yara, ciki harda wadanda basu wuce ‘yan shekaru biyar zuwa shida da haihuwa ba, wanda ta ce kuma za a yi musu horo na musamman kafin a sake su, su shiga cikin al’umma don gudun kyama da tsangwama.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama kan zargi rundunar sojan Najeriya da azabtar da kananan yara da kuma rike su ba tare da an tabbatar musu da laifinsu ba, wanda suka ce wasu lokutan har ya kan yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin su.

Sai dai irin wannan mataki da rundunar sojan ta dauka na sakin ire-iren mutanen ka iya kawo karshen wadannan zarge-zarge. Jami’in sojan da ya jagoranci mika mutanen da gwamnatin jihar Borno, Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya, yace yanzu haka sun mika adadin mutane 469 yayin da sauran 124 ke kan hanya bayan da aka gama tantance su.

Daraktan ma’aikatar Mata ta jihar Borno, Madam Ladi Clark Musa, wadda ta wakilci babbar sakataren ma’aikatar Hajiya Amma Abubakar, ta ce yanzu haka sun tanadi guraren da zasu ajiye mutanen da aka saka har sai an tabbatar da ganin zasu iya taimakawa kansu.

Domin Karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojan Najeriya Ta Saki Wasu Mutane 593 Da Aka Yi Zargin ‘Yan Boko Haram Ne - 3'30"