Boko Haram Ta Dauki Alhakin Kai Harin Masallacin Jami'ar Maiduguri

Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram wanda kuma ya bada sanarwar daukan alhakin kai harin Masallacin Jami'ar Maiduguri

A wani faifan da ya fitar ba tare da hotonsa ba, Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ya dauki alhakin kai hari cikin masallacin Jami'ar Maiduguri tare da shan alwashin kara kai har-hare har sai an tuba ana musulunci irin nasu

A jawabinsa wanda ya fara da jan aya daga Kur'ani Mai Tsarki Abubakar Shekau yace bam din da ya tashi jiya Litinin da safe 'yanuwansu ne suka tayar da fatan Allah ya karbi ran 'yan kunar bakin waken.

Yace Masallacin da aka tada bam din ba masallaci ba ne domin ana kafirci ciki ana hada masallaci da dimokradiya. Yace abun da ake yi cin amanar Annabi ne.

Inji Shekau zasu kara yi har sai an je lahira a tsaya gaban Allah a yi shari'a.

Ya kira duk wanda yake son yayi muslunci da gaske ya tuba ya bi akidarsu saboda su ne suke aikin Allah, suke yin addinin Allah tsantsa.

Game da Sambisa yace babu abun da ya samesu suna nan daram duk karya ake yiwa 'yan Najeriya.

Ya bada hujjar yin anfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake wanda ya hada da na baya bayan nan a Jami'ar Maiduguri.

Ga karin bayani daga sakon Abubakar Shekau.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram Ta Dauki Alhakin Kai Harin Masallacin Jami'ar Maiduguri - 6' 08"