Buhari Ya Sa A Kamo 'Yan bindigar Da Suka Fasa Gidan Yari A Imo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin a kamo a kuma hukunta dukkan 'yan bindigar da suka kai hari a gidan yari na Owerri, babban birnin jihar.

Umurnin na zuwa ne bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai garin na Owerri inda suka far wa gidan mazan da kuma wani sashe na hedikwatar ‘yan sandan jihar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda yanzu haka ya ke Landan domin a duba lafiyarsa, ya umarci dukkan hukumomin tsaron Najeriya da su yi amfani da dukkan hanyoyin da suke da su, domin kamawa tare da hukunta masu hannu a wannan aiki da ya kira na ta’addanci.

“Ya kuma ya bada umurnin a a yi maza a kamo dukkan fursunonin da suka tsere, wadanda mafi yawancinsu gaggan masu laifuka ne.” Kakakin Buhari Garba Shehu ya fada cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasra ta fitar a ranar Litinin.

Haka kuma, shugaba Buhari ya yi kira ga al’ummomin yankin da su taimakawa jami’an tsaro da bayanan da zasu kai ga kamawa tare da hukunta wadanda suka aikata mummunan aikin.

Da daren ranar Lahadi, wayewar garin ranar Litinin, wasu ‘yan bindiga suka kai hari babban gidan yari da ke garin Owerri na jihar Imo, tare da kubutar fursinoni sama da 1500.

Haka kuma maharan sun cinnawa hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar wuta a birnin na Owerri,inda suka kona kusan dukkan motocin da ke harabar.

Bugu da kari, ‘yan bindigar sun balle tare da sakin dukkan wadanda ake tuhuma da ke ajiye a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan.