Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata A Kafa Kotunan Musamman Don Hukunta ‘Yan Bindiga Da Masu Garkuwa Da Mutane - Obasanjo, Gumi


Makaman Da Yan Sanda Suka Kwace Daga Wasu Bata-Gari
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

Makaman Da Yan Sanda Suka Kwace Daga Wasu Bata-Gari

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Ahmad Gumi, sun yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta kafa kotuna na musamman don hukunta ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da mutane da suka mallaki makamai ba bisa ka’ida ba..

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan wata ganawar sirri ta tsawon sa'o'i biyu da suka yi a Abeokuta, tsohon shugaban kasa Obasanjo da Sheikh Ahmad Gumi sun bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da yiwa kasar katutu a kowane yanki na kasar.

Haka kuma sun ba da shawarar neman hadin gwiwar hukumar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS wajen shawo kan matsalolin tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa.

Ziyarar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a Plato
Ziyarar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a Plato

Obasanjo da Gumi sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba yiwuwar afuwa ga ‘yan bindiga da ke da niyyar tuba, tare da samar musu matsuguni da koya musu sana’o’in hannu tare da sama mu su ayyukan yi domin wanzuwar zaman lafiya.

Sun kuma jaddada bukatar gwamnati ta yi duk mai yiyuwa wajen zakulo miyagun 'yan ta'addar da ba su da niyyar tuba domin hukukta su a karkashin doka.

Sanarwar ta kara da cewa, matsalolin tsaro na neman su gaggari gwamnatin Najeriya kuma kamata yayi gwamnati ta dauki tsattsauran mataki tare da kai maganar a gaban kungiyar ECOWAS, domin samun maslaha.

Cif Olusegun Obasanjo da Sheikh Ahmad Gumi sun amince da su cigaba da hada gwiwa domin samar da mafita mai dorewa ga matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

A 'yan kwanakin baya dai Sheikh Gumi ya shiga wani rangadi a dazukan wasu jihohin Arewa maso Yamma, inda ya sadu da 'yan bindiga tare da zimmar shata tafarkin sulhu tsakaninsu da gwamnati.

Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga
Sheik Ahmed Gumi Tare Da Fulani Yan Bindiga

To sai dai matakin da malamin ya dauka ya hadu da kakkausan suka daga bangarori daban-daban na Najeriya, musamman a jiharsa ta Kaduna, inda gwamna Nasir El-Rufai ya ce sam ba zai yi sulhu da 'yan ta'adda ba.

Duk da haka kuma matakin ya sami karbuwa ga gwamnatin jihar Zamfara, daya daga cikin jihohin da ke fama da ayukan 'yan bindiga, inda gwamnan jihar Bello Matawalle ya dage akan yin sulhu da 'yan bindiga a jihar.

To sai dai duk da yake gwamnan na Zamfara na ikirarin samun nasara a shirin na sulhu, masu lura da al'amura na ganin cewa ba wani ci gaba da aka samu, ko raguwar ayukan 'yan bindiga a jihar ta Zamfara.

Amma duk da haka Sheikh Gumi a cikin sanarwar, ya mika goron gayyata ga Cif Obasanko zuwa jihar Kaduna don su ci gaba da tattaunawa kan neman mafita wanda Obasanjo ya amsa goron gayyatar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG