Cacar Baki Kan Shirin Tallafin Kudin Rarar Man Fetur

Matasa

Ana cigaba da cacar baki kan yadda ake gudanar da shirin kudin rarar man fetur ko SURE-P a takaice a jihar Taraba
Lokacin da gwamnatin tarayya Najeriya ta rage kudin tallafin man fetur ta yi alkawarin kafa wani shiri da yanzu ake kira SURE-P domin tallafawa matasa ta koya masu sana'o'i da tallfin kudin jari duk daga rarar kudin mam. Kowace jiha zata shirya abubuwan da ta san zasu taimaki matasa. Ita ma gwamnatin tarayya akwai abubuwan da zata rika yiwa matasa a duk jihohi kasar.

To sai dai a jihar Taraba shirintallafin kudin rarar man fetur ko SURE-P a takaice ya jawo cacar baki da yawa. 'Yan kungiyoyin dake da alaka da kokarin dawo da gwamna Danfulani Baba Suntai kan karagar mulki wanda yake jinya har yanzu da magoya bayan mukkadashin gwamnan Garba Umar sun shiga cacar baki kan yadda ake gudanar da shirin SURE-P a jihar. 'Yan gaba-gaban a komo da Danbaba sun ce ana nuna wariya a shirin tallafawa a jihar.

Mr. Danirl Yahana na Taraba Justice Forum ya yi zargin cewa na kusa da mukaddashin gwamnan da suke cikin gudanar da shirin suna nuna wariya wurin daukan matasa. Ya ce su basu gane yadda gwamnatin ke aiwatar da aikin ba. Dalili ke nan da suke yin korafi har ma sun mika takardar kokensu zuwa ga ICPC hukumar dake binciken cin hanci da rashawa da rashin tabbatar da adalci.

A martanin da ya mayar kan zargin nuna ban-banci Kwamishanan Matasa Habi Haruna Lau mai kula da shirin SURE-P a jihar ya ce lamarin ba haka yake ba Ya ce wasu ne suke ingiza wasu matasan amma tuni kwalliya ta soma biyan kudin sabulu a jihar a shirin. Ya ce babu wanda ya cika dari amma aduk fadin Najeriya babu wata jiha da ta fisu yin aikin da suka yi sai dai jihar Kano domin jihar ta yi wasu abubuwa da su basu yi ba. Ya ce sun horas da matasa sun kuma basu jari. Ya yi misali da wadanda suka yi aikin kiwon kaji da yanzu sun soma saka kwai.

Shugaban hadaddiyar matasa jihar Emmanuel George ya ce babu wani son kai ko wariya da gwamnatin jihar ta nuna. Idan akwai shi zai fiti fili ya fada.

Su ma kungiya nakasassu sun yaba da yadda ake gudanar da shirin to sai dai sun bukaci gwamnatin ta rika kulawa da su a wasu shirinta domin su ma suna da anfani.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Cacar Baki Kan Shirin Tallafin Kudin Rarar Man Fetur - 2:50