Accessibility links

Yayin da shekarar zabe ta 2015 ke karatowa wasu gwamnonin Najeriya `da zasu gama wa'adinsu sun soma kwadayin shiga majalisar dattawa da zara sun gama da ofishin gwamna

Wasu gwamnonin jihohin Njaeriya da zasu kammala wa'adinsu na mulki kamar yadda kundin tsarin kasar ya tanada sun soma hankoron zama sanatoci domin su shiga majalisar dattawa.

Duk da wai akwai sauran lokaci kafin zaben 2015 amma wasu 'yan siyasa sun soma shiri gadan-gadan domin lokacin. Wannan ya fito fili tsakanin gwamnonin dake zangon karshe na wa'adin mulkinsu.

A binciken da Muryar Amurka ta gudanar da yawan gwamnonin suna son su tsaya takarar sanato lamarin da ya fara kawo masu sabani da sanatocin dake cikin majalisar yanzu daga jihohinsu. Sanatocin da gwamnoninsu ke sha'awar tsayawa takarar mukamansu suna ganin ana son a kwace masu kujerunsu ne duk da korafin da wasu suke yi cewa majalisar dattawan ta kusa zama majalisar tsoffin gwamnoni.

To sai dai gwamnoni da yawa idan an takalesu da batun sai su ce ba haka ba ne. A jihar Kebbi gwamnan na son tsayawa sanata abun da wadanda suke da sanata yanzu sun ce a basu gwamna su kuma su bada sanata. To sai dai mai baiwa gwamnan jihar shawara a fannonin yada labarai Ibrahim Argungu cewa ya yi har yanzu gwamnan bai fito fili ya ce zai yi ko ba zai yi ba.

A jihar Neja sanatan da ake cewa kujerarsa ce gwamnan ke kwadayin samu ya fito fili yana caccakar gwamnansa. Ya ce idan ba an dawo an yiwa shugaban kasa biyayya ba talaka ne zai sha wuya. Su gwamnoni ba zasu sha wuya ba. Ya ce tun da ake ba'a taba samun talauci da fatara ba kamar yadda ake fama yanzu a karkashin gwamnatin jihar. Ya ce mutanen Neja suna cikin wulakanci da talauci da kuncin rayuwa, sun zama abun tausayi.

A jihohin Jigawa da Kano da Katsina da Bauchi babu irin wannan barakar domin gwamnoninsu basu fito sun nuna maitar tsayawa takara ba a fili duk da suna zangonsu na karshe.

A jihar Benue gwamnan da sanata mai ci yanzu sun shiga takunsaka. Amma a jihar Abia gwamna da sanata mai ci yanzu sun daidaita inda zasu yi musayar mukami. Haka ma a jihar Filato ba'a samu rashin jituwa ba.

Amma a jihar Akwa Ibom lamarin ya sha ban-ban domin an ji gwamnan yana shaidawa sanatoci da suka kai masa ziyara cewa shi ma yana fatan ya zama kamarsu a shekarar 2015 lamarin da ya haifar da rashin jituwa tsakanin gwamnan da sanata mai ci yanzu.

A jihohin Delta da Bayelsa duk labarin daya ne. Gwamnonin na son zama sanatoci. Sai da a jihar Rivers an ji gwamna Amaechi yanzu ya bar batun son zama mataimakin kasa zai tsaya takarar sanata.

Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.
XS
SM
MD
LG