China Ce Kasar Da Ta Fi Cin Zarafin 'Yan Jarida A Duniya

'Yan Jarida A Kasar China

Kungiyar 'yan jaridu ta duniya ta ce ‘yan jaridu a kalla 250 ne ke daure a fadin duniya, kuma mafi yawansu a China, a yayin da ake samun karuwar rikice-rikice tsakaninsu gwamnatoci kasashe da kuma kafofin watsa labarai masu zaman kansu, in ji kungiyar mai sa ido kan cin ‘yan jarida.

Da yawa daga cikin wadanda aka daure suna fuskantar tuhume-tuhumen "nuna adawa da gwamnati" ko kuma ana tuhumar su da samar da "labarai na karya", in ji rahoton da Kwamitin da ke New York wanda ke bayar da kariya ga ‘yan jarida.

Free Press

Kwamitin ya ambaci sunaye kasashen da aka fi samun cin zarafin ‘yan Jaridu a fadin duniya da suka hada da Turkiya da Saudiyya da Masar da Eritrea da Vietnam da kuma Iran.

Kungiyar da ke sa ido kan 'yan cin yan jaridu ta ce ta kirga a kalla 'yan jaridu 48 da aka daure a kasar ta China, inda aka samu ‘karin mutum guda fiye da na shekarar 2018, ya yin da Shugaba Xi Jinping ke ci gaba dsa kokarin dakile ayyukan kafofin watsa labarai.

-AFP