Trump: Ci Gaban Amurka Alheri Ne Ga Kasashen Duniya

Shugaban Amurka Donald Trump a taron tattalin arziki a Switzerland

Shugaban Amurka Donald Trump yace sa Amurka gaba da komi alheri ne ga sauran kasashen duniya, domin idan Amurka ta habaka sauran kasashe ma zasu habaka

Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya jajirce wajen kare matsayinsa na sa muradun Amurka gaba da komi, ya shaidawa taron tattalin arziki na kasashen duniya cewa,duniya zata amfana daga karfin tattalin arzikin Amurka, ya kuma yi kira ga kasashen su rungumi tsarinsa na bunkasa kasa.

Ya bayyana a cikin jawabin da ya yi na mintoci goma sha biyar a wajen taron tattali arziki na duniya da aka gunar a birnin Davos na kasar Switzerland cewa,"idan Amurka ta habaka, kasashen duniya ma zasu habaka".

Kamar yadda ya saba tun da ya shiga siyasa, Trump bai yi nadama ba kan tsawala kudin fice da wargaza yarjejeniyoyin harkokin cinikayya da kuma wadansu yarjejeniyoyin kasa kasa da aka cimma, da yake ganin suna kawo cikas a yunkurin habaka tattalin arziki.

Ikirarin sa Amurka gaba da komi ya janyo suka tsakanin masu halartar taron na Davos da dama, wadanda ke fifita daukar matakan habaka tattalin arziki na bai daya. Ba tare da ambaton Amurka ba, shugaban kasar Brazil Michel Temer ya yi amfani da jawabinsa a taron Davos ranar Laraba, ya bayyana adawa da abinda yake gani a matsayin yin kofar rago a tsarin cinikayya mara shinge da yace manyan kasashen duniya ke yi.