CIKI DA GASKIYA: Takaddama Kan Gonar Zinari a Damaturu - Kashi Na Biyu, 05 Afrilu 2022

Sarfilu Hashim Gumel

A makon da ya gabata ne muka sauka a Damaturu jihar Yobe inda Matashi Musa Umar a madadin sauran ‘yan uwan sa ya ce yake bin kadun wata babbar gona da a ka tabbatar a cikin ta akwai ma’adinai masu daraja dangin zinari.

Musa Umar ya ce sun sayarwa wani mutum rabin gonar su, su ka bar rabi don akwai zinari ko ma'adinai masu tsada a ciki da a ka tabbatar mu su.

Bayan haka Musa Umar ya ce su na zargin hakimin Damaturu da hada baki da wanda ya sayi rabin gonar don handame mu su dukiya.

A yi sauraro lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

Ciki Da Gaskiya: Takaddama Kan Gonar Zinari a Damaturu - Kashi Na Biyu - 9'58"