Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya: Takaddama Kan Gonar Zinari a Damaturu, 28 Maris 2022


Sarfilu Hashiim Gumel
Sarfilu Hashiim Gumel

A sabon shirin za mu sauka a Damaturu jihar Yobe, inda Matashi Musa Umar a madadin sauran ‘yan uwan sa ya ce yake bin kadun hakkin neman mallake mu su wata babbar gona da a ka tabbatar a cikin ta akwai ma’adinai masu daraja dangin zinari.

Musa Umar ya ce sun sayarwa wani mutum rabin gonar su, su ka bar rabi don akwai zinari ko ma'adinai masu tsada a ciki da a ka tabbatar ba wata tantama.

Bayan haka Musa Umar ya ce su na zargin hakimin Damaturu da hada baki da wanda ya sayi rabin gonar don handame mu su dukiya.

Sarkin Damaturu ya sa baki don a bi mu su hakkin su amma sun ce an hana su ganin Mai Martaba Sarki a halin yanzu.

A yi sauraro lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:11:09 0:00

XS
SM
MD
LG