Coronavirus: Adadin Mutanen Da Suka Mutu Ya Haura 1,800

A yau Litinin, Jami'an kiwon lafiya a China, sun tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus, ya zarce dubu saba'in, yayin da addadin wadanda suka mutu kuma, ya doshi kusan mutum 1,800.

Amma kimanin mutune dubu 11,000, da suka kamu da cutar sun warke.

Hukumomi a Lardin Hubei, na kasar China, inda cutar ta samo asali, sun ce, a yau Litinin, an samu karin mutum 100, da suka mutu, sanadiyyar cutar, yayin da karin wasu ma'aikatan lafiya suka isa yankin, don taimakawa fannin kiwon lafiyar da ya shiga wani hali tun bayan barkewar cutar a watan Disamba.

An dai tabo batun wannan babbar barazana, da cutar ta Coronanavirus, ke yi wa duniya, a babban taron tsaro, na kasa da kasa, da ake yi, a birnin Munich, da ke Jamus, inda shugaban hukumar Lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi tsokaci.

Darekta Janar Na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus

Ya ce, “Duniya na kashe biliyoyin daloli wajen yin shirin tunkarar hare-haren ta’addanci, amma, ba a kyakkyawan shiri kan barkewar wata cuta, wanda hakan hadari ne da zai shafi rayuka, tattalin arziki, siyasa, da al’amuran yau da kullum.”